Thursday

Home Buhari da Atiku sun bayyana jihohin da zasu rufe yakin Neman zabe a Yau Alhamis.

Buhari da Atiku za su gudanar da taron yakin zabe na karshe a yau Alhamis.


Mun samu cewa a yau Alhamis, 14 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasance dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, za su rufe taron su na yakin zabe.

Bisa ga tsari da bibiyar tafarki na doka da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta gindaya, a yau Alhamis shugaba Buhari zai rufe taron sa na yakin zabe a Mahaifar sa ta jihar Katsina, yayin da dan takara na jam'iyyar PDP zai rufe na sa a mahaifar sa ta jihar Adamawa.

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya tabbatar da cewa, tun a jiya Laraba tawagar shugaba Buhari ta sauka a birnin Katsinan Dikko, inda a yau zai bi sahunta domin gudanar da taron sa na yakin zabe.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, bayan girgiza magoya baya a mahaifar sa, shugaba Buhari zai shafe tsawon kwani uku a garin Daura domin kada kuri'ar sa yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar Asabar gabanin komawa fadar sa ta Villa dake garin Abuja a ranar Lahadi.

A yayin da jam'iyyar PDP ba za ta gudanar da taron yakin zabe ba a jihar Ogun, kazalika Wazirin Adamawa, zai rufe da taron sa na yakin zabe a yau Alhamis cikin birnin Yola wajen neman goyon bayan al'ummar Mahaifar sa.

Rahotanni sun bayyana cewa, a sakamakon dambarwa ta rikicin rabuwar kai a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun, ya sanya Atiku da kusoshin babbar jam'iyyar adawa ta kasa suka yanke shawarar janye taron yakin zabe a birnin na Abeokuta.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a jiya ne shugaba Buhari da kuma Atiku suka yi ido biyu da juna yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da duk yadda sakamakon zabe ya kasance tare da tabbatar zaman lafiya gabani da kuma bayan zaben na ranar Asabar.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments