Monday

Home Buhari Ya Samu Gagarumar Nasara A Kananan Hukumomi 13 Na Jihar Bauchi
Wakilinmu da ya kasance a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC a jihar Bauchi a cikin daren jiya Lahadi, ya shaida mana cewar an tattaro hadi da karanto sakamakon zaben shugaban kasa a wasu kananan hukumomin jihar Bauchi guda 14, inda ake tsumayar guda shida a safiyar nan.
Buhari yaci zabe

Sakamakon wanda ya nuna jam’iyyar APC ce ta samu gagaruman nasara a mafiya yawan kananan hukumomin jihar, inda sakamakon ya fito daga wajen manyan jami’an tattara sakamakon zaben a kowace karamar hukumar.

Wakilinmu ya shaida mana cewar kowani jami’in tattaro sakamakon zaben, zai yi bayanin abun da ya wakana a karamar hukumarsa bayan ya karanta sakamakon, inda zai kuma bayyana adadin kuri’un da aka kada, wadanda jam’iyyu suka yi nasara, da kuma kuri’un da aka samu marasa kyau da kuma wadanda aka kashe indan akwai.
Kasantuwar yanayin yadda sakamakon ya zo a tsakar dare, wakilinmu ya yi kokarin tattaro mana muhimman jam’iyyu guda biyu APC da PDP ne kawai, inda a sauran jam’iyyun za mu kawo bayaninsu a rahotonmu na gaba.

A cikin kananan hukumomi 14 da aka karanta sakamakonsu a hukumance, APC ce ke da rinjaye a kananan hukumomi 13, inda hakan ke nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya samu nasara a jihar Bauchi, a yayin da Atiku Abubakar ya samu karamar hukuma guda daya a cikin 14.

Sakamakon kananan hukumomi 14 na jihar Bauchi ga su kamar haka:
1. Karamar hukumar JAMA’ARE, Bauchi
APC = 20, 041
PDP = 4, 543
2. Karamar hukunar WARJI LGA
APC 19,570 ta samu kuri’un.
PDP 11,451.
3. Karamar hukumar ITAS GADAU:
APC 33,827
PDP 5,889
4. Karamar Hukumar GANJUWA:
APC 40,458
PDP 8,353.
5. Karamar hukumar DAMBAM da ke Bauchi:
APC. 22, 329
PDP. 3048.
6. Karamar hukumar MISAU
APC 35,393
PDP. 6,070
7. Karamar hukumar ALKALERI
APC. 45,200
PDP. 10,213
8. Karamar hukumar Bogoro
APC 5,284
PDP 23,664 (PDP ce ta yi nasara a wannan karamar hukumar).
9. Karamar hukumar KIRFI
APC. 22,035
PDP. 5,272
10. Karamar hukumar Giade
APC. 23,534
PDP 3,940
11. Karamar hukumar DASS
APC. 21,221
PDP. 6,413
12. Karamar hukumar DARAZO
APC. 37,327
PDP 6,911
13. Karamar hukumar TAFAWA BALEWA
APC. 36,931
PDP. 31,752
14. Karamar hukumar NINGI
APC. 54,095
PDP. 11,902.
Wakilinmu ya shaida mana cewar ya zuwa yanzu wadannan kananan hukumomi guda 14 ne aka kawo sakamakonsu hadi da karantasu a hukumance, inda a cikin kananan hukumomi 14 APC ta samu gagarumar nasara a kananan hukumomi 13 illa daya Bogoro da ta gagareta kawowa.
A bisa haka, hukumar zabe ta dage ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasar a jihar Bauchi zuwa karfe goma na safiyar yau Litinin domin ci gaba. Hakan ya faru ne a sakamakon rashin zuwan sauran kananan hukumomi shida a cikin daren jiyan.
KANANAN HUKUMOMI SHIDA DA BA A KAWO SAKAMAKONSU BA SUNE:
Karamar hukumar Bauchi, Toro, Zaki, Shira, Karagum, da kuma karamar hukumar Gamawa. Da karfe goma ne za a ci gaba da bayyana sakamakon sauran kananan hukumomi shidan a hukumance.

SOURCE LEADERSHIP.NG
No comments:
Write Comments