Friday

Home Da Dumi-Dumi : INEC ta kara ranakun karban katin zabe - Read more

INEC

Da Dumi-Dumi : INEC ta kara ranakun karban katin zabe - Read more


Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Takubu ya sanar da hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu a lokacin wani ganawa da kwamishinonin zabe. An yanke shawarar kara wa’adin ne bayan kwamishinonin zabe sun bayar da rahoto akan karban katunan zaben a jihohinsu daban-daban. Da farko, Legit.ng ta rahoto cewa akwai yiwuwar kara wa’adin karban katunan zabe kamar yadda hukumar INEC ta bayyana.

A baya mun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar ma yan Najeriya cewa za ta gudanar da zaben gama gari na 2019 kamar yadda ta shirya, don haka ba za ta dage zaben kamar yadda wasu yan siyasa ke kiraye kiraye ba. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar zabe a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja, inda yace duk da shari’un dake gaban kotu akan zaben fidda gwani na jam’iyyu, INEC ba zata dage zaben ba. Jaridar Legit.ng ta ruwaito Farfesa Mahmood ya dauki alkawarin ba zai saba ma umarnin kotu ba, kuma ba zai ji shayin sauke nauyin daya rataya a wuyansa ba.
“Kararrakin dake gaban kotu wanda suka samo asali dage zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasa sun kai guda 640."
No comments:
Write Comments