Sunday

Home Da duminsa: Buhari ya kayar da Atiku a mazabar Obasanjo ; Read more
Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya doke babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a akwatin zaben tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a zaben yau Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Yayin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri'u 87 a zaben shugaban kasar, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu kuri'u 18 ne kacal. Obasanjo dai ya goyi bayan Atiku ne inda ya rika bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi murabus daga siyasa.


Ku biyo mu domin karin bayani ...
No comments:
Write Comments