Wednesday

Home Dalilin Da ya hana mu sakin tubabbun ''yan boko haram 150 : Rundunar soji
Kwamandan sansanin ‘Operation Safe Corridor (OPSC)’ dake garin Mallam Sidi ta jihar Gombe , Kwanel Beyidi Martins, ya bayyana cewa, sun ki sakin tubabbun ‘yan kungiyar ta’addan nan na Boko Haram 150 ne saboda sake farfado da hare haren da aka samu a yankin Arewa maso gabas a ‘yan kwanakin nan. Haka kuma har yanzu ba a kammala cika ka’idojin dake tattare da sakin nasu ba har zuwa yanzu.

An sama da tsarin nan na ‘De-radicalization, Rehabilitation and Re-integration (DRR)’ don samar da yanayin sake shigar da tubabbun ‘yan Boko Haram a cikin al’umma, wannan kuma shiri ne da ya sanu asali bayan da hukumar tsaro na Nijeriya ta yanke shawara a watan Satumba na shekarar 2015. Fiye da ‘yan ta’adda 2,000 suka mika wuya tun da aka fara shirin, inda ko a makon da ta gabata an samu mutum 200 sun mika wuya a jihar Borno.

Kwanel Martins ya ce, ya zuwa yanzu an fuskanci ‘yan ta’adda 260 cikin su a kwai mutum 6 da suka fita dage hannun sojojin. An kuma salami mutum 95 a watan Fabrairu 2018 inda aka mika su ga jihohin su na Adamawa da Bauchi da Borno da kuma jihar Yobe, a halin yanzu suna nan suna ci gaba da harkokin rayuwarsu ba tare da wani matsala ba.

Kashi na karshe na mutum 150 sun kammala samun horonsu a ranar 24 na watan Nuwamba 2018 amma har yanzu suna nan a hannun mu saboda hare haren da ke samu a ‘yan kwanakin nan amman lallai za a sake su a kuma mika su ga jihohin su na haihuwa wanda sun nuna a shirye suke don karbar su tare da shigar da su a cikin harkokin al’umma da zaran an samu saukin hare haren.
An samar da sansanin OPSC tare da hadin gwiwar kungiyoyin kare hakkin bil adam na duniya da kuma dokokin kasa da kasa tare da kuma bin dokoki da tsarin mulkin Nijeriya, an kuma shirya shi ne don karya kadarin mayakan Boko Haram.

Kwamitin lura da harkokin shirin na OPSC ya hada da Shugaban Rundunar Tsaro na Nijeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin a matsayin shugaban kwamitin, haka kuma a kwai Gwamnonin Adamawa da Borno da kuma jihar Yobe, haka kuma a kwai shugaban rundunonin sojojin kasa da na sama da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya da Darakta a ofishin mai bayar a shawara a kan harkokin tsaro ‘National Security Adbiser’ da Darakta Janar na SSS da shugaban hukumar leken asirin kasa da kuma shugaban hukumar bayar da agajijn gaggawa na NEMA a matsayin ‘yan kwamiti.

Kwanel Martins ya yaba wa tsarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Janar Olonisakin da kuma shugabancin da jagoran farko na hukumar Manjo Janar BM Shafa ya bayar don tabbatar da kafuwar hukumar tunda farko.

Ya kuma kara da cewa, ana nan ana sa ido a kan dukkan mutane da aka saki an kuma samar da mutane 375 daga ofishin ‘National Security Adbiser’ da ‘Nigeria Prisons Serbice’ da ‘National Identity Management Commission’ da ‘Armed Forces of Nigeria’ da ‘Nigeria Police Force’ da ‘Department of State Serbices’ da ‘Nigeria Immigration Serbice’ da kuma ‘Nigeria Security and Cibil Defence Corps’ don taimaka wajen sa ido a kan tubabbun.

Sauran bangarorin da aka samar da jami’ai sun hada da ‘Federal Ministry of Women Affairs’ da ‘National Emergency Management Agency’ da ‘National Drug Law Enforcement Agency’ da ‘National Orientation Agency’ da ‘National Directorate of Employment’ da kuma ‘National Youth Serbice Corps’.

Ya kara bayyana cewa, a halin yanzu hankalin ‘yan Nijeriya ya fara karkata a kan harkokin hukumar OPSC bayan da aka samu bayanan dake nuna hannun tubabbun da suka samu horo a hare haren ta’addancin da aka samu a yan kwanakin nan.

A martaninsa ya ce, wadanda suke yin wannnan zargin ba su da cukakken bayanani na yadda hukumar OPSC ke gudanar da ayyukan su. Yana tattaunawarsa da ‘yan jarida a kan hanyarsa ta zuwa cibiyar samar da zaman lafiya na ‘Kofi Anan International Peace-keeping Training Institute’ dake Accra ta kasar Ghana.
Ya nisanta alaka a tsakanin ‘yan Boko Haram da tubabbun ‘yan Boko haram da suka tsira musamman ganin irin halin a yaba da suka nuna a zaman horaswa na makwanni 52 da suka samu a zaman sun a sansanin..

Ya kuma kara da cewa, sun kuma yi rantsuwa a gaban babban mai shari’a na kasancewa maus bin doka da oda, da kuma hanyoyin sa ido da muka sa musu, lallai babu yadda za su koma ga harkokin aiki tare da ‘yan Boko Haram.
Ya kuma kwatanta cibiyar ta OPSC da cewa, ita ce, daya tilo a Nijeriya inda ake yaki da ta’addanci ba tare da makami ba, kuma babu irinta a duk fadin Afrika, harkoin ta kuma ya yi dai dai da yadda ake gudanar da irin ta a fadin duniya.

SOURCE Leadership.ng
No comments:
Write Comments