Thursday

Home 'Dan majalissa a Turai ya rasa kujerarsa dalilin satar Burodi.
Mun samu labari cewa wani ‘dan majalisa a kasar Sulobania da ke cikin tsakiyar Nahiyar Turai, ya sauka daga kan kujerar sa, a dalilin satar burodi da yayi a wani shago lokacin da ya je cefane. Gidan jaridar BBC ta rahoto wannan labari.

Darij Krajcic ya rasa kujerar sa ne bayan ya dauki burodi a wani shago a cikin Garin Ljubljana watau babban birnin kasar Sulobania. Wannan ‘dan majalisa yace masu tsaron shagon sun ki kula sa ne lokacin da yake so ya biya kudin
Wannan ‘Dan majalisa, ya fadawa ‘yan jarida cewa ya dauko burodin nan na kwalama mai dauke da ganye da nama watau Sandwich, sai kuma ya iske ma’aikatan shagon su na yi masa yanga a sa’ilin da ya zo da nufin ya sallame su.

Mista Darij Krajcic dai ya faki idanun jama’a ya tsere daga shagon ba tare da biyan kudin wannan burodi ba. Sai dai daga baya ne ‘dan majalisar ya dawo da kan sa domin ya biya kayan da ya dauka yana mai bada hakuri cewa a yafe masa.

Babban ‘dan majalisar mai shekaru 54 a Duniya yace ya aikata hakan ne bayan ya bata lokaci ba tare da an mika masa na’urar POS na biyan kudi ba. Wannan ne fa ya sa jam’iyyun adawa su ka huro masa wuta inda shi kuma yayi murabus.

Wannan abu dai ya ba jama’a dariya, amma shi kuwa ‘dan majalisar na jam’iyya mai mulki a kasar Sulobaniya bai dauki lamarin da wasa ba. Krajcic yace ba a san ‘yan jam’iyyar sa da irin wannan abin kunya ba, don haka ya ajiye aiki.
No comments:
Write Comments