Thursday

Home Hajjin Bana : Hukumar NAHCON Ta Fara Tantance Jiragen Da Za Su Yi Jigila - 2019
Hukumar alhazai ta NAHCON ta fara gudanar da aikin tantance kamfanonin jiragen da za su yi aikin jigilar alhazai a shekarar 2019. An gudanar da bikin fara tantancewar ne a ranar Talata da ta gabata a Otal xin Stonehedge dake Abuja.
aikin hajjin bana,
 A wajen taron an kaddamar da kwamitin na musamman da aka xora wa aikin nazari tare da tantance takardar neman aikin jigilar da kamfanonin suka mika na bukatar sun a jigilar alhazai a shekarar 2019 daga Nijeria zuwa kasa mai tsarki. Fatima Usara, jami’ar watsa labarai na NAHCON, ta bayyana cewa, cikin aikin da kwamitin zai su gudanar sun hada da zavo kamfanin jiragen da za su yi jigilar alhazan Nijeriya da kuma jiragen kayan da za su kwashi kayayyakin alhazan daga kasa mai tsarki zuwa gida bayan kammala Aikin hajjin.

Ta ce, Shugaban kwamintin shi ne Alhaji Modibbo Saleh, Kwamishina mai kula a tsare tsare a hukumar NAHCON, an kuma jawo sauran yan kwamitin ne daga hukumomin kwastam da hukumomin yaki da cin hanci na kasa da kuma ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma wakilai daga hukumomin alhazai na jihohi.

 A jawabinsa na bude taron, shugaban hukumar NAHCON, Abdullahi Muhammad, ya bayyana wa ‘yan kwamtin cewa, an zabo su a bisa amana da amincewa, ya kuma kamata su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata don a samu gabata da akin hajji na bana ba tare da wanu matsala ba. Ta kuma ce wadanda suka yi jawabi a wurin taron sun hada da shugabar kwamitin majalisar Dattija dana Wakilai a kan harkokin kasashen waje, Monsurat Sunmonu da Nnenna Ukeje. 
No comments:
Write Comments