Saturday

Home Hotuna : Yanzu Yanzu obasanjo ya kada kuri'arsa.

Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya kada kuri'arsa a mazabarsa da ke ward 11 unit 22 a harabar gidan Olusomi da ke Abeokuta a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa.

An dai fara kada kuri'a a mazabar ne tun sa'o'i uku da suka gabata a yawancin mazabu da ke jihar ta Abeokuta.

A hirar da ya yi da manema labarai gabanin jefa kuri'arsa, Obasanjo ya yi kira ga al'umma su fito kwansu da kwarkwata su jefa kuri'arsu domin zaban shugabanin da za su jagorance su.
No comments:
Write Comments