Friday

Home Hotuna - Ziyarar Shugaba Buhari a jihar Adamawa -: Mahaifar Atiku Abubakar.
A ranar jiya Alhamis, 7 ga Watan Fabrairu, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Adamawa don hidimar yakin neman sake zabe.
‘Yan kwanaki kadan kafin zaben shugaban kasa, Buhari ya ziyarci Jihar dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, mutanen Jihar Adamawa sun fito makil sun mamaye ko ta ina don nuna goyon bayan su ga shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Haka kuma kun sani cewa Atiku Abubakar ma ya ziyarci Jihar Katsina a ranar alhamis shi ma, inda rahoto ya bayyana cewa jama’ar Jihar Katsina sun fito kwansu da kwarkwata don bayyana goyon bayan su ga Atiku ga zabe na gaba.

HOTUNAN BUHARI A ADAMAWA.
Ga Kuma. HOTUNAN AKITU A KATSINA

Abin mamaki anan shine, Atiku ya samu marabtar mutane da yawa a Jihar shugaba Buhari, Katsina. Haka kuwa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan jama’ar Jihar Adawa da yawan kwarai dagaske, watau garin Atiku dan takaran Jam’iyyar PDP.
No comments:
Write Comments