Wednesday

Home Jinin "yan Nigeria bai cancanci zuba ba saboda takara :- ATIKU yayin ganawarsu da Buhari.
Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, yace kudirin takararsa bai cancanci zubar jinin kowani dan Najeriya ba.

Abubakar wanda yayi Magana a wajen taron shiga sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, ya ari furucin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonatan na 2015, inda ya jero muimmancin zabe na lumana da gaskiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a nasa martanin ya jadadda kira ga hukumar zabe mai zaman kanta akan zabe na gaskiya da amana.
Shugaban kwamitin zaman lafiya, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya kuma yi kira ga hukumomi tsaro dasu zamo tsaka-tsaki a lokacin zaben ranar 16 ga watan Fabrairu da kuma 2 ga watan Maris.
No comments:
Write Comments