Saturday

Home Kai tsaye - Yadda zabe yake kasancewa a jihar kano.
Mu na samun labari cewa ana sayen kuri'ar Talakawa yayin da ake kan layi na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar tarayya a jihar Kano. Kano ce inda APC ta fi samun kuri'a a zaben da aka yi a shekarar 2015.


Jaridar The Cable ta bada rahoto cewa ana biyan mutane kudi domin su zabi jam'iyyar da ake so a yankin Mandawari da ke cikin karamar hukumar Gwale. Kamar yadda mu ka ji ana raba N500 ne ga masu shirin kada kuri'a.
Mun kuma ji labari cewa rikici ya barke tsakanin jama'a da kuma Ma'aikatan tsaro a akwatin zaben da ke cikin wata makarantar sakandare da ke cikin Gwale a jihar ta Kano. A wasu wuraren kuma na'rurorin aikin zaben ba su aiki.

Tun cikin tsakar dare aka fara hawa layin zabe a Kano

Wasu masu lura da aikin zaben 2019 a Najeriya sun bayyana cewa na'urar da ake amfani da su wajen tantance masu kada kuri'a sun gaza aiki a cikin Garin Madobi. Wannan ya sa aka yi watsi da na'urorin a Yankin Kanwa da ke cikin Madobi.
Kamar yadda labari ya zo mana, Matan aure da jama’a sun soma ajiye layi ne tun kusan karfe 2:00 na dare a cikin karamar hukumar Gwarzo da ke cikin yankin Arewacin jihar Kano, su na jiran ma’aikatan zabe su karaso cikin safiya.

Haka zalika kuma mun samu labari cewa da sanyin safiya Ma'aikatan zabe sun fara shirin gudanar da aikin zabe a Yankin Bunkure da ke cikin Jihar ta Kano. Jami’an zabe sun shigo yankin ne dai tun karfe 7:00 domin su karbi kayan aiki.
Bayan nan kuma mun ji cewa ana shirin fara zabe a cikin yankin Ginsawa da ke karamar hukumar Tofa. A akwatin zabe na 004 da ke cikin mazabar na Ginsawa, tun sa’a guda da ta wuce aka fara niyyar gabatar da zaben na shugaban kasa.
No comments:
Write Comments