Wednesday

Home Kin amincewa da sakamakon zabe: Abubuwa 6 da Atiku ya fadi a jawabinsa
Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rashin gamsuwarsa da sakamakon zaben 2019 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta fitar a ranar Laraba 27 ga watan Fabrairu.


Atiku ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben kana akwai kurakurai cikin alkalluman da INEC ta wallafa, hakan yasa ya ce zai garzaya kotu domin a bi masa hakkin sa.

Atiku ya yi jawabi da 'yan Najeriya a yau kuma ga muhimman abubuwan da ya fadi a cikin jawabin.

1 - Atiku ya mika godiyarsa da dubban al'ummar Najeriya da suka fita kwansu da kwarkwata domin kada kuri'unsu yayin zaben shugabancin kasar na 2019.

2 - Ya yi ikirarin cewa akwai makarkashiya da aka shirya na magudi a wasu johohi masu yawa wadda hakan yasa ba zai amince da sakamakon da aka fitar ba.

DUBA WANNAN: Adam A Zango ya taya Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu (bidiyo)

3 - Atiku ya ce bai amince da adadin kuri'un da aka samu a wasu jihohin da rikicin Boko Haram ya tarwatsa su ba inda wai har sun dara na johihin da ake zaune lafiya.

4 - Ya yi ikirarin cewa anyi amfani da sojoji wurin musgunawa masu kada kuri'a musamman a jihohin Rivers, Akwa Ibom, Imo da wasu jihohin wadda hakan abu ne da ya yi kama da yanayi na mulkin kama karya na soja.

5 - Atiku ya ce da ya sha kaye a zabe na adalci ne da ba zaiyi wata-wata ba wurin kiran wanda ya lashe zabe domin ya taya shi murna kuma ya bayar da gudunmarsa wurin hada kan kasa musamman gyara alaka tsakanin Arewa da Kudu.

TRY YOUR SONG FOR FREE
TRY YOUR SONG FOR FREE
TRY YOUR SONG FOR FREE

6 - Daga karshe Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben kuma ya dau alwashin zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben.

DUBA WANNAN : WAKOKIN HAUSA , SABBIN WAKOKIN RARARA
No comments:
Write Comments