Sunday

Home Mataimakin Gwamna Bantex ya gaza kawowa APC akwatin sa a Jihar Kaduna
Arch. Barnabas Bantex ya samu kuri’a 2113, yayin da shi kuma ‘dan takarar PDP wanda shi ne yake kan mulki ya samu kuri’u 2, 301. Malamin zaben yankin watau Yusuf Emmanuel shi ne wanda ya sanar da wannan sakamakon.

Manema labarai dai sun kawo labari cewa Bala Bantex ya lashe akwatin da yake zabe da kuri’a 227 inda ‘dan takarar PDP ya iya samun 15 kacal. Sai dai bayan an hada kuri’ar yankin gaba daya, APC ta sha kaye a hannun APC.

A zaben shugaban kasa kuma shugaba Muhammadu Buhari na APC ya samu kuri’a 1, 443 inda shi kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP ya tashi da kuri’a 2, 991. Yanzu mu na cigaba da jiran sakamakon yankin.

Yanzu haka dai Sanata Danjuma La’ah ne yake kan kujerar inda yake neman komawa majalisar dattawa domin ya wakilci Mazabar Kudancin Kaduna. Kusan dai ba a samun wanda yake yin tazarce a wannan kujera a Kaduna.

A zaben majalisar tarayya, PDP ta samu 2,056 yayin da APC ta samu kuri’a 1,641. Jam’iyyar UPN ta samu 243, PRP 191 sai kuma jam’iyyar adawa ta SDP ta iya tara kuri’a 50. Ana cigaba da kirga zaben jiya a jihar.
No comments:
Write Comments