Saturday

Home Mu sha Dariya: Labarin Lado da Tanko Dariya Dole
Mu sha Dariya: Labarin Lado da Tanko Dariya Dole.LADO yana zaune, a kusa da Abokin sa TANKO. Sai LADO yace:- Kai duniya ana abubuwan mamaki. .
Sai TANKO yace:- Me kuma ya faru...?

 Sai LADO yace:- Wai ina zaune,kusa da wata kwata, saiga wata Mata mai ciki tazo zata tsallaka.

Sai naji dan cikin nata na cewa:- Ina kwana Baba...! Sai Matar nan ta lura, sai tace mun, kana kamada Babansa shiyasa ya gaidakai.... 

Sai shima TANKO yace:- Mhmmm... Yo wannan har abun mamaki ne...?

 Nida aka yima abunda na kusa zaucewa. .

 Sai LADO yace:- Wane abune...?

 Sai TANKO yace:- Wai tun daga Kaduna direban motar mu ya rasu, amma bamu saniba, sai da mukazo Kano... Mun je gidan mai, anan aka tambayeshi na nawa za'azuba...?

 Sai aka ga ashema Direban ya rasu, harma ya tsandare...!

 Sai LADO Yace, Wallahi karyane dan Ubanka!!! 
No comments:
Write Comments