VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Saturday

Home PDP - Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe.


PDP  - Fadar shugaban kasa ce ta sa aka dage zabe.Tayi ikirarin cewa fadar shugaban kasa ce da shirya dage zaben sai dai ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zai sha kaye nan da kwanaki kadan. Jam'iyyar adawar ta kuma yi ikirarin cewa har yanzu fadar shugaban kasar tana cigaba da shirin yadda za ta janyo wasu cikas ga hukumar zabe INEC ta yadda ba za a gudanar da zabukkan a rana guda ba.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mr Kola Ologbondiyan a cikin jawabin da ya yi a taron manema labarai da jam'iyyar ta kira domin tofa albarkacin bakin ta a kan dage zaben.

A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja inda zai hallarci wani taron da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shirya zaben na Najeriya. Ana sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a ranar 23 ga watan Fabrairu yayin da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi kuma za a gudanar da shi a ranar 9 ga watan Maris.

SOURCE @LEGIT.NG
No comments:
Write Comments