Friday

Home Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)
Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)Wani bidiyo ya billo inda Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bukaci mutanen jihar Kwara da sub a shugaban kasa Muhammadu Buhari kaso 90% na kuri’unsu.


NAN ta ruwaito cewa an nadi bidiyon ne a Ilorin a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu, ranar karshe na gangamin yakin neman zabe.

Saraki ya kasance darakta-janar na kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar.

Bisa ga dukkanin alamu tiuntuben harshe Saraki ya samu a wajen gangamin domin wata murya ta gyara masa furucin nasa inda tace ‘Atiku’.

Shugaban majalisar dattawar na gwagwarmayar ganin ya dawo kan kujerarsa na majalisar dattawa inda yake karawa da abokin adawarsa na jam’iyyar All Progressives Congress Ibrahim Oloriegbe. Oloriegbe ya sha alwashin fatattakar Saraki zuwa gida.
No comments:
Write Comments