Friday

Home Wanda musulmai yakamata su zaba ya shugabance su ranar Asabar - Wani malami a Zariya
Malamin dake zaune a garin Zariya ya kuma shawarce su da su yi anfani da iliminsu da kuma sanin da suka yi na sanin yadda shugabanci ya ke, da su zabi ‘yan takara nagari a duk zabukan da za a yi a wannan shekara ta 2019.

Haka zalika Shehin malamin ya kuma yi kira ga duk wani shugaba da wakilai da aka zaba ko kuma da za a zaba, da su rike amanar da aka dora ma su, domin shirin amsa tambayoyin da za a yi ma su a gobe bayan sun sauka daga matsayin da aka zabe su.

Sheikh Malam Abdulhakami Kumasie ya ci gaba da cewar, babbar matsalar da ta ke addabar siyasa a wannan lokaci da ake ciki, shi ne rashin samun shugabanni da kuma wakilai nagari da suke tunanin al’ummar da suke wakilaci da kuma shugabanci.

KU KARANTA : Zaben 2019: Za A Yi Jidali Idan Baki Suka Yi Mana Katsalandan | cewar el-Rufai  

A nan ne Malamin addinin musuluncin ya kara da cewar, mafiya yawan wadanda ake zaba a wannan lokaci, da kuma wadanda aka zaba a ‘yan shekarun baya, babu tunanin wadanda suka zabe su, sai dai tunanin kansu a madafun ikon da suke, tun daga jiha ya zuwa tarayya.
No comments:
Write Comments