Friday

Home Wasu mahara sanye da kakin soji sun kai farmaki kan kayan zabe. A jihar benue.
Hukumar zabe ta inec ta tabbatar cewar a ranar Laraba wasu "yan bindiga sanye da Kayan Soji sun kaiwa motar hukumar da ke dauke da kayayyakin na zaben 2019 a jihar benue,  INEC din ta tabbatar cewar, yan bindigar sun kaiwa motar  farmaki ne a lokacin da take tsaka da tafiya da kayyakin da za'a gudanar da zaben ranar asabar a yankin Logo na jihar Benue.

Kwamishinan zabe a jihar, Dakta Nentawe Yilwatda, shi ne ya shaida hakan wa ‘yan jarida a lokacin da ke yi wa ‘yan jaridan bayanin shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun kasa a gobe Asabar.

Kamar yadda yake cewa, motar da aka kai wa harin tana dauke ne da kayyakin gudanar da zabe kanana da aka ware domin yin zabe a Logo da ke ckin jihar.

“Ba da jimawa ba (a ranar Larabar nan) motarmu da ke dauke da kayyakin gudanar da zabe aka kai mata hari a hanyar Logo. Maharan da suka kai farmakin suna sanye ne da kakin sojoji,” In ji shi.
No comments:
Write Comments