Monday

Home Wasu manyan jami'an APC sun koma PDP a wata jihar Arewa24.
Wasu manyan jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da daruruwan magoya bayansu daga karamar hukumar Jos South na jihar Plateau sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin hadewa da Shugaban kwamitin doka da kasuwanci a majalisar wakilai, Hon. Edward Pwajok (SAN).

Mai ba APC shawara akan doka, Hon. Joseph Mani, wanda ya jagoranci masu sauya shekar ya bayyana cewa sun bar APC ne saboda jam’iyyar bata da abun ba yan Najeriya.

Yace: “Mun koma PDP ne don marawa Hon. Edward Pwajok wajen kawo wa Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a PDP, dan takarar gwamna na jam’iyyar Sanata Jeremiah Useni, da kuma dukkanin yan takarar PDP kuri’u da yawa a jihar Plateau.
 “Mun yi ammana cewa shugabancin Atiku da Useni a matsayin gwamna a jihar Plateau, zai inganta rayuwar yan Najeriya sannan ya kawo zaman lafiya ta yadda yan gudun hijira a jihar Plateau za su koma gidajensu. APC babu komai cikinta sai tarin yaudar, a kullun suna cikin korafi saboda jam’iyyar bata da abun nunuwa."

 Pwajok yace idan aka zabi Atiku, yunwa, rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki duk za su zamo labara sannan naira zai dawo da daraja, yayinda tattalin arzikin Najeriya zai inganta.
Wani tsoon ministan matasa da wasanni da kuma Shugaban PDP a jihar Platau, Hon. Damishi Sango, wanda ya tarbi masu sauya shekar a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Plateau, yace PDP ce kadai jam’iyyar da ta damu da tsaro da jin dadin mutanen Plateau.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments