Monday

Home Yadda aka hallaka mutane 66 a cikin kwana biyu a jihar kaduna.
PREMIUM TIMES ta samu karin cikakkun bayanan da suka tabbatar da cewa an kashe mutane 66 a Karamar Hukumar Kajuru, kamar yadda Gwmnatin Jihar Kaduna ta bada sanarwa.


An kai harin ne tun ranar Litinin, kuma hari ne na ramuwa, wanda aka kai wa wasu can baya.
Wannnan karin nayani ya fito fili ne bayan da aka rika waswasin cikakken abin da ya faeru.
Gwamna Nasir El-Rufai ne ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ba shi rahoton samun gawarwaki har 66, kuma ya yi sanarwar a jribirin zabe.
Wannan dalili ne ya sa mutane da yawa suka dauka cewa a ranar Juma’a din aka yi rikicin.
Gwamnan ya ce wasu batagari ne suka kashe su, yayin da suka kai musu hari a yankunan Maro Gida Iri, cikin Karamar Hukumar Kajuru.
Ya ce rugagen da kisan ya faru a cikin su, sun hada da: Rugar Bahago, Rugar Daku, Rugar Ori, Rugar Haruna, Rugar Yukka Abubakar, Rugar Duni Kadiri, Rugar Shewuka da Rugar Shuaibu Yau, inji shi.
Sai dai kuma gwamnan bai bayyana jami’an tsaron da suka ba shi rahoton kisan ba.
Chidi Odinkalu na Hukuamr Kare ‘Yancin Dan Adam da jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna duk sun yi tababar kisan, saboda babu wani sahihin karin bayani daga bangaren gwmnati.
Amma kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa El-Rufai ya yi wannan jawabi ne bisa rahoton da Operation Yaki suka bas hi a sirrrance. Oeration Yaki ya kunshi ‘yan sanda, Sojiji da kuma SSS.
Rahoton jami’an Operation Yaki da suka raka wasu Fulani cikin rugagen su, sun samu gawarwaki har 66, ciki har da na kananan yara 22 da mata 12.
Wakilin PREMIUM TIMES a jihar ya zanta da wasu.
Benjamin Maigari, wanda ya ce ya je yankin ne domin ya yi zabe. Ya ce an kai hare-hare ne guda biyu. Na farko kabilar Adara ne aka kai wa harin. Na biyu kuma harin ramuwar gayya ne a kan Fulanin.
Sai dai kuma ya ce harin ramuwar gayyar shi ne ya fi cin rayuka da dama.
Ya ce harfin da aka kai wa kabilar Adara a ya ci rayuka 11 tun a ranar Litinin.
Ya kara da cewa su kuma kabilar Adara sun yi zargin cewa Fulani ne suka kai musu hari, sai kawai suka tashi a cikin daren suka shiga kashe Fulani a cikin rugagen su.
“Harin da aka kai wa Adara an kashe mata da kananan yara. Haka na Fulanin an kashe mata da kananan yara da dawa.”
Ya ce jami’an ‘yan sanda sun je a washegari, domin su tantance irin barnar da aka yi. Sun gana da Hakimin Kajuru da kuma DPO na Karamar Hukumar Kajuru.

SOURCE PREMUIMTIMES
No comments:
Write Comments