Sunday

Home YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.* Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayinneman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayintaakan abunda yake wajibi ko mustahabbi akan ka;kamar neman zabin Allah akanyin azuminramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitarda zakka,azumin alhamis da litimin da dai sauransu.

* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan suncikaro, misali: mutum ne yake son yaje umra karona biyu a lokaci guda kuma yana so yaje watakasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allahakan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.

* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikinlamarin sa, to ba zai yi nadama ba Insha Allah.Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].

* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yanakoya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) acikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkunta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibati amrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaana thumma raddini bihi."
Da Harshen Larabci

MA'ANA

"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshenlamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]

* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannankarantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafankarya don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace

* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.

* Wannan Addu'a ta istarawa ana yin tane bayanka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].

* Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah.

* Haka kuma babu wani hadisi da yazo dagaAnnabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masabayani al-amarinsa.

* Babu shakka duk wanda yayi zai samu natsawucikin abunda Allah madaukakin sarki ya zabamasa.

* Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutanedayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayinnutsuwar zuciya, idan aure ne sai kajizuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar.

* Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita nedaga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Anayin tane koda lokacinda aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana dagacikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili".

* Wannan kenan don gane da abunda ya shafiSallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Ayki Abundamuke rubutawa da karantawa Ameen.

ALLAH YA TAIMAKE MU Ameen
No comments:
Write Comments