Thursday

Home Yadda Boko haram suka bude wuta akan tawagar gwamnan borno a hanyarsu ta yakin Neman zabe.
Yadda Boko Haram su ka bude wa tawagar kamfen din Gwamnan Barno wutaAkalla Boko Haram sun kashe mutane biyar, ciki kuwa har da soja daya, a wani kwanton bauna da suka yi wa tawagar kamfen din Gwamna Kashim Shettima na Jihar Barno.

Kakakin Yada Labarai na gwamnan, Isa Gusau, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da kai harin, amma bai fadi adadin barnar da aka yi wa tawagar ba.

An kai musu hari ne a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa kamfen kan titin Maiduguri zuwa Gambu, hanyar da ke fita har zuwa cikin kasar Kamaru.

TAFIYA KAMFEN DA DARE

Wanda ya shaida harin a kan idon sa, ya ce a cikin daji ne aka yi wa tawagar kwanton-bauna aka bude mata wuta, cikin kauyukan da ke kan hanyar zuwa kan iyaka da kasar Kamaru.

Gwamna Shettima ya na takarar sanata, kuma shi ne daraktan kamfen na yakin neman zaben gwamna, wanda Babagana Umara ke takara.

Wata majiya ta kuma shaida wa PREMIUM TIMES cewa tawagar ta fita ne da niyyar tafiya Gamboru-Ngala da yammacin Tatala, da niyyar su kwana a wani gari da ke kusa da kan iyaka, wanda dakarun Boko Haram sun taba mamaye shi.

Boko Haram sun bude wa tawagar gwamna wuta jim kadan bayan da tawagar ta wuce kauyen Logomani, wanda ke kilomita 20 tsakanin sa da Dikwa.

YADDA AKA BUDE WA TAWAGAR WUTA

Kamar yadda wasu dakarun sa kai na CJTF, wadanda akasari sun fi yawa a cikin jami’an tsaron da ke tafiya rangadi da gwamnan, sun bayyana cewa Boko Haram sun kai harin ne a cikin wasu motoci biyu masu budadden baya, irin wadanda ake girka wa manyan bindigogin nan tashi-gari-barde.

“Yan Boko Haram din nan duk sun yi shiga irin ta sojoji, kuma sun ajiye motocin na yaki guda biyu a gefen titi.”

Majiyar ta ce Boko Haram sun tsaya ba su ce komai ba, har sai da suka bari kusan rabin motocin kamfen sun wuce, ciki har da motar da gwamna ke ciki ita ma ta wuce. Daga nan su ma sai suka shiga motocin na su, su ka bi jerin gwanon motocin kamfen.

“ Saboda mu fa da farko mun dauka sojojin gaske ne, domin har daga musu hannu muka rika yi, kuma wani daga cikin su da ke saman mota daya shi ma ya rika daga mana hannu. Dukkan su kuma sun a sanye da kayan sojoji sannan kuma fentin motocin na su ma irin na sojojin kasar nan ne.

Daya daga cikin CJTF ya kara shaida cewa bayan da maharan na Boko Haram suka shiga cikin sahun jerin gwanon motocin kamfen, an rika tafiya tare da su har tsawon kilomita 5, inda daga nan kuma sai suka kara gudu, kara yin wa motocin da ke bayan su tazara.

“Ko da mu ka fahimci sun kara gudu, sai kuma motocin biyu suka raba hanya, daya ta rika gudu daga gefen hagu, daya kuma daga dama, sun sa hanya tsakiya, sai kawai na cikin motar suka juyo suka rika bude wa motocin da ke bayan su wuta.”

Majiyar ta bayyana cewa yawancin wadanda abin ya shafa, ‘yan CJTF ne wadanda ke biye da tawagar daga baya.

“Ba ka ganin komai sai tashin kura, domin hanyar ba ta da kwalta, saboda kowa ya rude ya kama gaban sa, har da mu ‘yan CJTF.”

Majiyar ta kara da cewa soja dayan da aka kashe shi ne wanda ya tsaya tsayin daka ya rika bude wa Boko Haram wuta, da nufin sauran jama’a su samu damar arcewa cikin daji.

Ya ce an kashe mutane hudu, ciki har da sojan daya, sannnan kuma wasu da dama sun bace a cikin jeji ba a san inda suke ba.

BOKO HARAM SUN KWACE MOTOCIN KAMFEN 10

“Akalla motoci 10, ciki har da motar daukar dakarun CJTF Boko Haram suka kwace a farmakin da suka kai wa tawagar kamfen ta Kashim Shettima.

“Amma kuma an tsinto wasu gawarwaki biyu a yau Laraba, yayin da wadanda suka tsere cikin daji, har da Babban Sakatare daga baya sun bayyana bayan sun gaji da yawo a cikin jeji.”

Sauran magoya bayan APC da suka koma Maiduguri da yammacin Laraba, sun ce sauran tawagar gwamna da ta yi gaba, sun wuce har Gamboru-Ngala inda suka kwana, daga nan suka ci gaba da kamfen a tsawon ranar Laraba.

GWAMNA BAI BI SHAWARAR SOJOJI BA

Wasu dakarun CJTF sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa tun da farko sai da sojojin da ke Dikwa su ka gargadi gwamnan cewa kada su karasa har Gamboru-Ngala da jijjifin almuru.

Dikwa na kilomita 73 tsakanin garin da Maiduguri, ya nan hanyar Gamburo-Ngala.

“Da farko ma sojojin cewa suka yi ba za su bude mna hanya mu wuce ba, saboda karfe 6 na yamma ta wuce, kuma Boko Haram kan kai hare-hare a daidai wancan lokacin.

“Amma duk da haka sai masu gudanar da kamfen din suka nace cewa sai sun wuce. An yi ta sa-in-sa mai zafi a tsakanin su da sojoji, har dai sai da gwamna da kan sa ya sa baki, ya ce a bude hanyar.

“Daga nan sai sojojin suka rika guna-guni, amma dai suka bude mana hanya. Sai dai kuma ba su yi mana rakiya ba.”

An kai harin ne daidai wajen kauyen Logomani, wata mabuyar Boko Haram da ta yi kaurin suna wajen yawan kai farmaki. Ta na kilomita 22 daga Dikwa.

Tawagar gwamna ta koma Maiduguri misalign 7 na yammacin Laraba, bayan ta gudanar da kamfen a Mafa da Dikwa.

Majiya ta ce har aka kammala kamfen din, gwamna Shettima bai ambaci labarin kai musu hari a kan hanyar su ta zuwa ba.

SOURCE PREMIUMTIMES
No comments:
Write Comments