Sunday

Home ‘Yan adawa sun bankado kutungwilar da akayiwa Shugaban hukumar zabe : INEC
Kakakin kungiyar ta ‘yan adawa, Imo Ugochinyere yake cewa an shirya korar Mahmood Yakubu daga bakin aiki inda ake neman maye gurbin sa da Amina Zakari wanda ita ce mafi girma a cikin kwamishinonin hukumar INEC.

Ugochinyere yake cewa gwamnatin Buhari tana neman tayi amfani da dakatar da zaben da aka yi a matsayin dalili na yin waje da shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, domin a nada Hajiya Amina Zakari.

Mai magana da yawun bakin na kungiyar CUPP yayi tir da yadda shugaban kasar yayi gum game da yadda jami’an tsaro da babban bankin CBN na kasa wadanda su ke karkashin sa su ka rika kawowa INEC cikas kwanan nan.

Kungiyar tayi ikirarin cewa shugaban na INEC ya ki amincewa da a gudanar da zabe a wasu wurare tare da dakatar da zaben wasu yankin jiya, wanda zai bada damar a tafka magudi, don haka ake kokarin a tsige sa daga kan kujerar na sa.
CUPP ta gargadi gwamnatin shugaba Buhari ta guji aikata wannan aiki domin kuwa dokar kasa ba ta bata dama ba. Kwanan nan ne shugaban kasar yayi waje da babban Alkalin Najeriya wanda kungiyar tace ya sabawa tsarin mulki.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments