Wednesday

Home "Yan sanda sunyi nasarar damke kasurgumin mai garkuwa da mutane a katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Katsina, jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan a wata takardar manema labarai da jami’in ya saki yau Laraba a garin Katsina.

Kasurgumin mai garkuwa da mutanen ya yi wa wani dan kasuwa barazanar cewa zai yi garkuwa da shi, in har bai biya Naira miliyan biyu ba, mutumin mai suna Magaji Gudaji mai shekaru 30, wanda ke zama a kauyen ‘Yandoka dake Dayi a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar cafke shi ne bayan da suka samu bayanan sirri, inda suka same shi da wayar hannu kirar Itel da kuma layin wayar da yake amfani da shi wajen aikata laifukkan, rundunar ta ga sakon barazanar da ya aike wa da wancan dan kasuwan, kuma tuni ya amsa laifin nashi ma.

Rundunar ta ce da zarar ta kammala binciken ta za ta gurfanar da mutanen a gaban kotun don fuskantar hukuncin da ya dace da shi, sannan tana ci gaba da aikin gano sauran abokan aikata laifin shi Magaji din.
No comments:
Write Comments