Wednesday

Home Yanzu Yanzu: APC ta haramtawa PDP taron kamfen cikin garin Abuja.

Da sansdin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, akwai yiwuwar samun cinkoson al'umma tare da jerin gwanon Motoci yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban na jam'iyyar APC da za a gudanar a yau Laraba cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

A yayin da a yau babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta shirya gudanar da taron ta na yakin neman zaben kujerar shugaban kasa cikin garin Abuja, jam'iyya mai ci ta APC ta yi kakagida wajen tilastawa jam'iyyar ta hamayya janye na ta taron da kudirci gudanarwa. APC za ta gudanar da taron yakin zabe a garin Abuja, PDP ta janye na ta.


Jam'iyyar PDP na ci gaba da zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke jagorancin kasar nan a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC da mulki na kama karya yayin da ta haramta ma ta gudanar da taron ta cikin garin Abuja a makon da ya gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an tsananta tsaro a garin Abuja yayin da jiga-jigan jam'iyyar APC na kasa da kuma gwamnonin kimanin 22 na jam'iyyar za su halarci taron yakin neman zabe yayin da shugaban kasa Buhari zia gabatar da jawaban sa a yau 13 ga watan Fabrairu.

 Masu sharhi akan harkokin siyasa sun yi zargin cewa, jam'iyya mai ci ta APC ta shirya gudanar da taron ta na yakin zabe a yau cikin garin Abuja domin haramtawa jam'iyyar adawa PDP gudanar da na ta taron a babbar fada ta shugabancin kasar nan.

SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments