Saturday

Home Yanzu-Yanzu Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu ya sha alwashin karban sakamakon zabe Shugaban kasa idan har aka yi zabe da gaskiya.

Ya yi Magana ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabar Ajiya da ke Jimeta, Yola.
Atiku ya sha alwashin amincewa da sakamakon zabe idan har aka kamanta gaskiya

Atiku yace a matsayinsa na dan damokradiyya, bashi da matsala wajen karban sakamakon zabe.

“Ni dan damokradiyya na gaskiya ba kamar wasu ba,” inji shi.

Atiku wanda yayi jawabi ga manema labarai bayan kada kuri’arsa ya jadadda cewa koda dai yana da tabbacin yin nasara, zai amshi kaye idan har zaben ya zamo babu murdiya a ciki.

Ya nuna jin dadi ga yadda masu zabe suka fito don sauke hakkin da ya rataya a wuyansa a lokacin zabe tare da fatan dukkanin jami’an zabe za su gudanar da ayyukansu cikin amana.
No comments:
Write Comments