Wednesday

Home Yanzu-Yanzu :- Buhari zai gana da Atiku, za su kulla wata muhimmiyar yarjejeniya

Yanzu-Yanzu :- Buhari zai gana da Atiku, za su kulla wata muhimmiyar yarjejeniya


Jaridar Daily Trust  ta rawaito cewa, a yau Laraba dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma dan takara na jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari, za su rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya tare da amincewa da duk yadda sakamakon zabe ya kasance.


shugaban kasa Buhari da babban abokin adawar su za su gana a yau cikin garin Abuja domin tabbatar da wannan yarjejeniya dangane da sakamakon zaben kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

A yayin tuntubar fadar shugaban kasa dangane da wannan babban lamari, mai magana da yawun shugaban kasa Buharim Mista Femi Adesina ya bayar da tabbacin cewa Ubangidan sa zai halarci taron na kulla aminci kan sakamakon zaben bana.

Kazalika, babban hadimi na musamman ga tsohon mataimakin shugaban kasa akan hulda da al'umma, Mista Paul Ibe, ya ce ba bu abinda zai hana Atiku rattaba kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da tawakkali kan duk yadda sakamakon babban zaben ya kasance.

Sannan shugaban kasa Buhari da sauran 'yan takara masu hankoron kujerar shugaban kasa, sun rattaba hannu tare da kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a ranar 11 ga watan Dasumba na shekarar da ta gabata.
No comments:
Write Comments