Saturday

Home Yanzu-Yanzu Hukumar INEC tana ganawa da masu ruwa da tsaki akan zabe.

Yanzu-Yanzu Hukumar INEC tana ganawa da masu ruwa da tsaki akan zabe.Hukumar INEC dai tana ganawa da masu ruwa da tsakin ne, bayan da ta yanke hukuncin dage zaben kasar har zuwa mako mai zuwa, a cikin kasa da awanni biyar kafin fara gudanar da zaben.

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa dage zaben ya biyo bayan kyakkyawan tunani da kuma dabaru na gudanar da aiki, da kuma kudurinta na gudanar da sahihin kuma kammalallen  zabe, wannan ne dalilin da ya sa hukumar ta ga cewa idan har ta gabatar da zaben a wannan halin da ake ciki, yace dage zaben zai baiwa hukumar damar maganin duk wasu matsaloli da ka iya afkuwa yayin gudanar da zaben da kuma tabbatar da cewa anyi zaben cikin tsari ta yadda kowa zai gamsu ya amince da sakamkonsa.

"Hakika wannan mataki ne mai wuyar dauka, amma yin hakan ya zama wajibi domin ganin cewa hukumar ta gudanar da sahihin zabe da zai tabbatar da dorewar demokaradiyyar kasar." a cewar sa.
"Hukumar a yanzu ta dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabreru, 2019.
"Haka zalika, zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da kuma na cikin babban birnin tarayya Abuja zai gudana a ranar Asabar 9 ga watan Maris, 2019.
No comments:
Write Comments