Monday

Home Zaben 2019: Atiku ya yi nasara a jihar Adamawa
Mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a jihar Adamawa yayin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fidda sakamakon babban zaben kasa na ranar Asabar.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya kare martabar mahaifar sa ta jihar Adamawa yayin da ya lallasa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Gamayya ta jimillar gami da kididdigar sakamakon zaben kamar yadda hukumar INEC ta fitar ta tabbatar da cewa, Atiku ya lashe adadin kuri'u 410,267, yayin da shugaban kasa Buhari ya samu kuri'u 378,072 kacal.
Atiku yayin yakin zaben sa a jihar Adamawa
KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno
Karamar hukumar Hong
APC: 20,471
PDP: 23,039
Karamar hukumar Ganye
APC: 20,360
PDP: 17,770
Karamar hukumar Guyuk
APC: 10,825
PDP: 22,059
Karamar hukumar Lamurde
APC: 8,123
PDP: 21,404
Karamar hukumar Yola South
APC: 34,534
PDP: 20,414
Karamar hukumar Mubi South
APC: 19,361
PDP: 10,514
Karamar hukumar Mubi North
APC: 26,746
PDP: 23,156
Karamar hukumar Shelleng
APC: 13,531
PDP: 11,912
Karamar hukumar Girei
APC: 17,765
PDP: 14,673
Karamar hukumar Yola North
APC: 43,865
PDP: 27,789
Karamar hukumar Numan
APC: 10,610
PDP: 23,469
Karamar hukumar Demsa
APC: 6,989
PDP: 29,997
Karamar hukumar Mayo-Belwa
APC: 20,842
PDP: 23,734
Karamar hukumar Madagali
APC: 8,208
PDP: 14,594
Karamar hukumar Maiha
APC: 17,034
PDP: 7,916
Karamar hukumar Song
APC: 17,350
PDP: 22,648
Karamar hukumar Fufore
APC: 29,507
PDP: 16,430
Karamar hukumar Gombi
APC: 12,805
PDP: 18172
Karamar hukumar Jada
APC: 21,332
PDP: 22,877
Karamar hukumar Michika
APC: 10,669
PDP: 32,085
Karamar hukumar Toungo
APC: 7,145
PDP: 5,614
No comments:
Write Comments