Tuesday

Home Abun-da-babba-ya-hango: Buhari yayi fatali da kudurorin doka 2 daga majalisar tarayya.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi fatali da wasu kudurorin dokoki guda biyu da majalisar tarayya suka kai masa domin ya sa masu hannu, kamar dai yadda kakakin majalisar wakilan, Yakubu Dogara ya bayyana a zauren majalisar ta wakilai.

Buhari yasha kunu


Kudurorin da shugaban kasar ya wancakalar din dai sun hada da na kafa wata cibiya da zata rika koyar da hanyoyin lalubo matsaloli da kuma gyaran Najeriya watau Chartered Institute of Training and Development of Nigeria.

KU KARANTA: Tsaffin Jakadun Najeriya sun nemi a soke maimacin zaben gwamnan wata jiha a Arewa, sun fadi abinda zai haifar.

Haka ma dai shugaban kasar ya yi fatali da saka hannu a kan dokar da ta shafi kafa wata manazartar harkokin aikin ceto na sararin samaniya watau Nigerian Aeronautic Research Rescue Bill.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ba wannan ne karon farko ba da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya ki sa wa wani kuduri daga majalisar hannu ba a 'yan kwanakin nan.

A kwanan baya ma dai shugaban kasar ya yi fatali da wani kudurin da yayi gyare-gyare a harkokin zabe.
No comments:
Write Comments