Wednesday

Home An Haramta Jigila Da Jirage Kirar Boeing 737 MAX A Nijeriya Bayan Hatsarin Jirgin Kasar Habasha
Hukumomin Nijeriya sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen haramta jigila da jigragen sama kirar Boeing 737 Max, hukumomin Nijeriyan sun yi hakan ne don tsare rayuka da dukiyar al’ummar kasar,
Air crashes in ethopia, air accident in ethopia.

ministan sufurin saman Nijeriya Sanata Hadi Sirika ne ya bayyana hakan, bayan kammala taron majalisar ministoci da ake duk mako.

Haramcin zai ci gaba har sai an kammala binciken hatsarin jirgin sama kasar Habasha da ya yi hatsari a karshen makon da ya gabata, jirgin Habashan kirar Boeing 737 Max, duk babu wani kamfanin jirgin sama da yake amfani da wannan kirar jirgin, amma hukumomin sun haramta kirar jirgin ma wucewa ta sararrin samaniyyar Nijeriya gaba daya.

‘Hukumar da take kula da jiragen fasinja ta Nijeriya, ita ma ta fitar da takardar haramci ga dukkan kamfanonin jigilar jiragen sama, inda ta bayyana cewa kada wani kamfani ya yi amfani da jirgin wajen sauka ko tashi a dukkan filayen jirgin da ke a fadin kasar nan.’ Inji Sirika
No comments:
Write Comments