Sunday

Home Baki har kunne: Buhari ya daɗaɗawa tsagerun Neja Delta, sun yi ma sa jinjina ta ƙin ƙarawa
Domin ramawa Kura kyakkyawar aniyyar ta, kungiyar tsaffin tsagerun Neja Delta, ta yi jinjina tare da yabawa alheri da kuma kwazon gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakamakon biyan albashin su na wata akan kari.

Jagoran kungiyar ta tsaffin masu tayar da kayar baya a yankin Neja Delta, Godstime Ogidigba, shi ne ya kwarara wannan yabo ga shugaban kasa Buhari yayin wata sanarwa a ranar Lahadi cikin birnin Benin na jihar Edo.

Tsagerun naija delta
Farfesa Charles Dokubo


Mista Ogidigba ya ce kungiyar ta yanke shawarar antaya lambar yabo bisa ga nagartaccen jagoranci na Farfesa Charles Dokubo, babban mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Buhari akan harkokin Neja Delta.

Ya ce kungiyar ta yabawa kwazon gwamnatin shugaban kasa Buhari da kuma Farfesa Dokubo a sakamakon biyan albashin tsaffin tsagerun Neja Delta na kowane wata akan kari da kuma bayar da tallafi na musamman ga Matasan su domin dakile zaman kashe wando.

KARANTA KUMA: Na Yi Kuskure Da Na Shiga Siyasa, Yanzu Na Tuba – Adam Zango.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta shimfida shirin afuwa ga tsaffin tsagerun Neja Delta da suka ajiye makamai, kungiyar su a halin yanzu na ci gaba da cin moriya gami da samun alherai na gwamnatin biyo bayan sulhu da ke tsakanin su.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments