Tuesday

Home Buhari na goyon bayan mika wa 'yan Kabilar Ibo mulki a 2023 - Okwara
Wani jigo na jam'iyyar APC, Cif Livinus Okwara, cikin bayyana aminci da kuma kyautata yakinin sa, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai gaza ba wajen goyon mika akalar jagorancin kasar nan a hannun 'yan kabilar Ibo a 2023.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Cif Okwara ya ce shugaban kasa Buhari ba zai kosa ba wajen mika akalar jagorancin kasar nan a hannun 'yan kabilar Ibo duk da rashin samun goyon bayan yankin su na Kudu maso Gabashin kasar nan yayin babban zaben kasa na 2019.
Cif Okwara ya ke cewa, kasancewar shugaban kasa Buhari adalin jagora, a shekarar 2023 zai jajirce wajen ganin akalar jagorancin kasar nan ta koma hannun 'yan kabilar Ibo da tarihi ya tabbatar yankin su na Kudu maso Gabashin Najeriya bai taba samar da shugaban kasa ba.

Yayin ci gaba da ganawa da manema labarai na jaridar The Nation, Cif Okwara ya yi kira ga 'yan siyasar yankin Kudu maso Gabashin kasar nan da su hada kawunan su tare da kasancewa tsintsiya madauri daya wajen cin gajiyar kujerar shugaba Buhari a 2023.

KARANTA KUMA: 'Yan kabilar Ibo sun ce a basu kujerar Saraki a majalisar dattawa  

Ya kuma kalubalanci kungiyar zamantakewa da al'adun kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, dangane da gazawar ta wajen kare martabar al'ummar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, inda ya ce ba bu abinda ya kamata a halin yanzu face a yi watsi da ita.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kungiyar Ohanaeze Ndigbo reshen jihar Legas, ta bayyana aminci gami da goyon baya kan dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.
No comments:
Write Comments