Wednesday

Home Da duminsa: Gwamna El-Rufai ya samu goyon bayan kungiyar matasan Arewa
Kungiyar matasan Arewa (AYF) ta goyi bayan takarar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tana mai bayyana shi a matsayin wanda ya fi cancanta ya ci gaba da mulkin jihar.


Kungiyar AYF reshen jihar Kaduna, a cikin wata sanarwa daga hannun kodinetanta, Abba Ismail, ta yi kira ga matasa da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabar gwamnan jihar Nasir El-Rufai karkashin jam'iyyar APC.

Kungiyar AYF ya ce gwamna El-Rufai ya nuna cikar kamalarsa ta zama shugaba wanda ya zama wajibi a yaba masa, musamman kokarinsa na ganin cewa an dakile matsalar tsaro a jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce: "Kungiyar AYF ta jinjinawa matasan Nigeria kan yadda suka nuna dattako a yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru da kuma fatan za su maimaita hakan a zaben gwamnonni da na 'yan majalisun dokoki da za a gudanar Asabar mai zuwa.
"A wannan gabar, muke kiran dukkanin mambobin kungiyar AYF da ke a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben Mallam Nasiru El-Rufai saboda irin ci gaban da ya kawo da kuma dakile matsalolin tsaro a jihar.
"Hakika ko a iya haka, gwamnan ya cancanci yabo da kwatantawa a matsayin misali na shugaba na gari da kuma sanin hanyoyin raba romon demokaradiyya a birni da kauyukan jihar Kaduna. Tabbas, El-Rufai ne wanda ya fi cancanta ya ci gaba da mulkin jihar."
No comments:
Write Comments