Monday

Home Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace babban basarake a kudancin Najeriya
Punch ta ruwaito cewa wasu maza dauke da makamai wanda adadin su ya kai biyar ne su kayi kutse cikin fadar basaraken a sanyin safiyar ranar Asabar.
Yan bindiga

An ce sun ta harbe-harben harsashi a iska kafin su kayi awon gaba da Enogie zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wata majiya daga kauyen ta ce 'yan bindigan sun bankawa motarsu wuta kafin suka tasa keyar basaraken cikin motarsa kirar Nissan Sunny suka tafi da shi.
An gano cewar sun kama hanyar jihar Delta da basaraken.


DUBA WANNAN : Hukumar 'yan sanda ta bayyana matakin da za ta dauka kan harin da aka kai jihar Kaduna


Enogie dai tsohon sufritandan 'yan sanda ne da ya gaji mahaifinsa da ya rasu wasu shekaru da suka gabata.
Kakakin yan sandan na jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar ya yi da majiyar Legit.ng inda ya ce tuni sun fara bincike a kan lamarin.
"Eh, da gaske ne, Yan sanda sun fara bincike a kan lamarin domin tabbatar da cewa an kwato basaraken cikin koshin lafiya," inji shi.
No comments:
Write Comments