Sunday

Home Dalilin da ya sa ba mu yi abin da Buhari yace a Kano ba – inji Kwankwaso
Sanatan Kano ta tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, yayi hira da ‘yan jarida a jihar Kano yayin da ake shiryawa zaben gwamna da za a karasa a jihar. Sanatan ya tattauna kan batutuwan siyasar Kano.
Tsula, abba k yusuf, andussalam gwarzo, kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi magana game da abin da ake ta magana a kai bayan an yi ram da wasu manya a gwamnatin Ganduje mai-ci, wanda ya kira da barayin akwatin cikin gwamnati.

Injiniya Rabiu Kwankwaso ya bada labarin yadda yayi ram da wadanda su kayi kokarin tarwatsa tattara kuri’un karamar hukumar Nasarawa, tsohon gwamnan yace da kan sa ya je ya sha gaban wadanda ake zargi da wannan aiki.

Sanata Rabiu Kwankwaso yace mutanen sa ba su harbe wadanda ake zargi da satar akwatin zabe bane saboda ganin irin adalcin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar don haka yayi kokarin mika su gare sa domin ayi hukunci na gaskiya.

DUBA WANNAN :- Hukumar 'yan sanda ta bayyana matakin da za ta dauka kan harin da aka kai jihar Kaduna .

Kwankwaso ya yaba da halin kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Babban Sanatan na PDP yayi wannan bayani ne a lokacin da ya gana da wasu ‘yan gidan rediyo a gidan sa, yana mai bada tabbacin cewa jam’iyyar adawa ta PDP za ta karbe mulki daga hannun gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje mai-ci.

Babban ‘Dan siyasar ya nuna cewa Kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Wakili, jami’i ne mai mutunci da kuma adalci. Sai dai wasu daga cikin masu rike da madafan iko a gwamnatin Kano su na ganin CP Wakili ya nuna son kai a lamarin sa.

A baya shugaban kasa Buhari dai ya nemi jami’an tsaro su bindige duk wadanda aka kama su na kokarin satar akwatin zabe. Injiniya Kwankwaso yace sanin adalcin ‘yan sanda ya hana su yin hakan.
No comments:
Write Comments