Sunday

Home Jerin sunayen gwamnonin da EFCC za ta tuhuma kan rashawa da zaran mulkinsu ya kare -
Gabanin ranar 29 ga watan Mayu, ranar da zababbun gwamnoni da yan majalisu za su karbi ragamar mulki da wakilci, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta kafa wani kwamiti da zai binciki wasu gwamnoni da akai zarginsu da cin hanci da rashawa.
Ganduje video

Jaridar Punch ta ranar Lahadi ta ruwaito cewa akalla jihohi 12 ne za su samu sabbin gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu bayan karewar wa'adin gwamnonin da ke ci a yanzu. Jihohin sun hada da Lagos, Ogun, Oyo, Imo, Kwara, Nasarawa, Yobe, Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Zamfara.
Daga cikin gwamnoni 12, guda hudu daga cikinsu ana zarginsu da cin hanci da rashawa.

Gwamnonin sun hada da Rochas Okorocha na jihar Imo; da gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed; da shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari; da gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun.

KARANTA WANNAN : Tsaro: Mazauna Zamfara sun fara neman asirin tsarin kai daga mafarauta da 'yan tsibbu, hotuna

Okorocha wanda jam'iyyar APC ta dakatar da shi, ana zarginsa da karkatar da N1bn da nufin daukar nauyin yakin zaben surukinsa, Uche Nwosu, wanda ya tsaya takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar AA.

A jihar Zamfara kuwa, EFCC na binciken Yari da karkatar da makudan kudade da suka kai biliyoyin Nairori. A shekarar 2017 EFCC ta zargi Yari da bayar da umurnin kwashe N500m da kuma $500,000 na Paris Club, inda Yari ya yi amfani da N500m wajen biyan bashin da bankin 'First Generation Mortgage Limited' ke binsa.

Gwamna Ahmed na jihar Kwara kuwa, zai gurfana ne gaban EFCC da zaran wa'adin mulkinsa ya kare bisa zarginsa da wasu mukarraban gwamnatinsa na karkatar da akalla N1bn mako daya kafin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Shi kuwa Amosun, wanda shi ma jam'iyyar APC ta dakatar da shi zai shiga komar hukumar EFCC da zaran ya sauka daga mulki. Ana zarginsa da karkatar da akalla N4bn karkashin shirin bayar da ranche ga manoma, 'Anchor Borrowers' da gwamnatin tarayya ta turawa manoman jihar Ogun.
No comments:
Write Comments