Monday

Home INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano
Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe ne, Bello Shehu ya bayyana haka a yau Litinin, 11 ga watan Maris.
Kano state result, sakamakon zaben kano, abba gida gida, ganduje yaci zabe

Hakan ya biyo bayan hargitsa cibiyar tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Nassarawa da ita kadai ta rage, da aka yi cikin daren jiya Lahadi.

Ya ce idan suka yin haka ne za su bayyana sakamakon da doka ta amince a karba, da wanda doka ba ta amince a karba ba.
Jami’in tattara bayanai na jihar Kano, Farfesa Shehu ya ce ma’akatan sa na duba kuri’un da aka soke, wadanda ya ce suna da yawa.
Daga nan ya ce za su tantance a cikin kuri’in su gano yadda za a samu karancin su.
KU KARANTA KUMA: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi . 
Ya ce ta haka ne za a iya gano wanda ya yi nasara.

Shi kuma Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, na Jihar Kano, yace a inda suka gano cewa akwai ko an yi zabe ba da ‘card reader’ ba, to sifili za a bayar a kawai a wuce wurin, a ci gaba da aiki.
No comments:
Write Comments