Monday

Home Ka san duk magudin da APC ke shirya wa, PDP ta kafa hujja da kalaman Buhari.
Babbar jami'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ce kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cewar ba zai saka baki a zabukan da za a maimaita a wasu jihohi ba sun tabbatar da cewar ya yarda an tafka magudin zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu. PDP ta bayyana cewar kalaman na shugaba Buhari wani salo ne na janye hankalin jama'a daga magudin da jam'iyyar APC ke shiryawa a zaben da za a yi a jihohi 6 ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

pdp buhari

Jam'iyyar PDP na wannan kalamai ne a cikin wani jawabi da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai, ya fitar a yau, Litinin. Ologbondiyan ya kara da cewa kalaman Buhari dake bayyana cewar wasu mambobin APC na matsa ma sa lamba kan ya sa baki domin a yiwa 'yan takarar ta alfarma ya isa jama'a su fahimci yadda jam'iyyar ta kware a bangaren tafka magudin zabe.

"Idan 'yan Najeriya basu manta ba gabanin zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya, shugaba Buhari ya dauki alkawarin za a yi zabe sahihi na gaskiya amma sai ga shi jagororin jami'iyyar APC sun yi amfani da 'yan daba da jami'an tsaro domin hana jama'a fito wa su kada kuri'a a yankunan da basu da yawan magoya baya.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Sanata Akpabio ya garzaya kotu kan faduwa zaben sa 

"Shugaba Buhari ba zai iya wanke kan sa daga zargin magudi ba domin mun san cewar babu wanda yake bawa sojoji umarni sai shugaban kasa,"
a cewar Ologbondiyan. Kazalika, PDP ta yi kira ga dakarun soji da su nesanta kan su daga wuraren zabe tare da jan hankalin hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta tabbatar ta bawa jama'a abinda suka zaba musamman a jihohin da PDP ta bawa APC tazarar kuri'u.
No comments:
Write Comments