Saturday

Home Kai-Tsaye: Yadda zaben gwamna na raba gardama ke gudana a jihar Sokoto
SAKAMAKON ZABE DAGA RUMFUNAN ZABE

- Bello Issa 012, Sokoto South LGA, Sokoto
APC 187
PDP 133
- PU 004, Waziristan B Ward,
Sokoto North LGA
APC 156
PDP 135

Al'umma sun koma gefe guda suna jira yayin da jami'an zabe suka fara kirga kuri'u a rumfunan zabe na Buida Bakintiti 002 a karamar Hukumar Denge Shune na jihar Sokoto.
Sakamakon zaben jihar sokoto

An fara kada kuri'a a rumfar zabe mai lamba 003 a mazabar Rafi B a karamar hukumar Sokoto misalin karfe 8.27
Zabe yana tafiya yadda ya kamata a karamar hukumar Sokoto ta Arewa
Zabe yana tafiya lafiya kalau a Hubare 004 (PU), a karamar hukumar Sokoto ta Arewa inda aka fara jefa kuri'a misalin karfe 8 da rabi na safe.

An fara samun rashin jituwa a rumfar zabe
Duk da cewa ba a fara kada kuri'a ba, an fara samun rashin jituwa tsakanin wakilan jam'iyyu a rumfar zabe mai lamba 12 (Sarkin, Adar, Atiku) inda jami'in zaben ya ce na'urar card reader da aka bashi bata aiki yadda ya kamata.

Bayan zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihohin Najeriya, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta bayyana cewa zabe bai kammalu a wasu jihohi shida ba, jihohin sun hada da Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Plateau and Sokoto.

Hukumar ta dauki matakin ne saboda sashi na 34 (e) na dokokin zabe da ya ce zabe ba zai kammala ba idan tazarar kuri'un da ke tsakanin dan takarar da ya lashe zabe da mai biye masa ba su dara adadin kuri'un da aka soke ba.

DUBA WANNAN : Zaben Kano: Sakamakon zaben cike-gurbi na Gwamna Ya fara fita. 

Wannan dalilin ne yasa INEC ta zabi ranar 23 Maris domin gudanar da zaben raba gardama.

A jihar Sokoto dai jam'iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri'u 3,412 a zaben ranar 9 ga watan Maris. A yau kuma za a gudanar da zabe a mazabu 135 a kananan hukumomi 22 na jihar inda ake sa ran mutane 75,403 za su kada kuri'a.

A wannan shafin zamu rika kawo muku yadda zaben raba gardamar ke kasancewa a jihar Sokoto.
A halin yanzu rahoton da muka samu daga Punch na nuna cewa an fara kada kuri'u a rumfar zabe mai lamba 004 da ke Rijia a jihar Sokoto.
No comments:
Write Comments