Monday

Home Kotu ta soke takarar Abba Kabir Yusuf na PDP a Kano.
Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta rushe zaben da jam'iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam'iyyar.

Alkalin kotun, Lewis Allagoa ya yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta PDP ba ta gudanar da zaben cikin gida ba, saboda haka kotun ta rushe zaben. Dan takarar gwamnan a jam'iyyar ta PDP, Ali Amin-little, ne dai ya shigar da karar yana kalubalantar yadda aka yi zaben da har Abba Kabir Yusuf ya zama dan takara.

DUBA WANNAN : Yadda APC ke shirin amfani da sojoji domin murde ma na zabe –PDP

Abba Kabir ne dai dan takarar jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, babban mai hamayya da gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar APC. Bayan kotun ta soke takarar Abba, yanzu ta ba jam'iyyar PDP mako biyu da ta gudanar da zaben fitar da dan takara. Wannan na zuwa ne, yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha a Najeriya. Karin bayani na tafe...
SOURCE BBCHAUSA
No comments:
Write Comments