Wednesday

Home Kujerar kakakin majalisar Kasa: Dogara ya ja baya daga tseren
Alamu sun nuna cewa ba lalllai be kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sake neman matsayin da yake kai ba a yanzu.
Yakubu dogara

Hakan baya rasa nasaba da sahihan abubuwan da ke kewaye da jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP), a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar da aka kammala.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar wacce ta dawo hutu ta dage zamanta zuwa ranar Laraba domin karrama abokan aikinsu da suka rasa ransu, Hon. Temitope Olatoye Shuga, daga jihar Oyo da kuma Hon. Bethel Amadi daga jihar Imo.

Da yake magana da jaridar Independent, wani majiyi da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa ba zai sake Neman kujerar kakakin majalisa ba a majalisar kasar na yara.

Ku tuna Dogara ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki a watan Satumban 2018 ya nemi kujerar takara na wakiltan mazabunsu Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi a karo na biyu, bayan sun babe da gwamnan jihar Mohammed Abubakar kan banbancin siyasa.
No comments:
Write Comments