Saturday

Home Malamin addinin da ya yi hasashen faduwar Buhari Amma yanzu ya sake magana
Babban malamin addinin nan na kirisa mai da'awar Annabta watau Udoka Daniel Okechukwu dake zaune a jihar Anambra da yayi hasashen cewa dan takarar shugabancin kasa a PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zaben 2019 ya sake magana.

Fasto Udoka ya bayyana cewa duk da dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta bayyana akasin abun da shi ya hasaso amma dukkan alkaluman sa na cigaba da nuna cewa Atiku din ne dai ya lashe zaben.

Legit.ng Hausa ta samu cewa ya kuma bayyana shakkun sa akan sakamakon zaben da INEC ta sanar inda ya ce ta yaya za'a gudanar da zabe ranar Asabar amma ba a fadi sakamako ba har sai ranar Laraba wanda hakan ne ya nuna wa duniya cewa an yi magudi.
Ya cigaba da cewa shi hasashen sa har yanzu akan gaskiya yake kuma yana kira ga masu sukar sa da su yi duba akan yadda zaben ya gudana. Ya kara da cewa kawai dai hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) ce ta aikata ba dai dai ba.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments