Friday

Home Sanatoci 64, yan majalisar wakilai 151 ba za su dawo majalisa ba
A wannan Zabe da ya gabata APC ta kafa mafi rinjaye a majalisar dattawa, akalla sanatoci masu ci 64 da mambobin majalisar wakilai 151 ne ba za su dawo majalisar dokokin kasaar ba a raanar 9 ga watan Yuni da za a rantsar da sabbin shiga.


Sanatoci 45 kawai ne da kimanin mambobin majalisar wakilai 209 ne za su dawo majalisar tarayyar kasar.

15 daga cikin sababbin sanatocin da aka zaba sun kasance tsoffin gwamnonin jiha.
42 daga cikin sanatoci 64 da ba za su dawo ba sun rasa kujerarsu ne tun a watan Oktobar shekarar da ta gabata a zaben fidda gwanin jam’iyyunsu. Sauran 22 sun sha kaye ne a zaben majalisar dokoki da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

A majalisar wakilai, adadin yan majalisa da ba za su dawo ba ya wakilci kaso 41.9% nay an majalisar 360. Ana sanya ran adadin zai karu yayinda har yanzu ba a kaddamar da sakamakon wasu mazabu ba.
Sai dai sakamako da aka saki zuwa yanzu ya nuna cewa APC ta samu sama da mambobi 200 a majlisar yayinda PDP ke da akalla sama da 100.

KU KARANTA KUMA: (Music) Sabuwar wakar rarara Munshiga Next Level mp3 Download.

Daga cikin manyan wadanda suka fadi zaben akwai Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya kasance a majalisar tun 2011. Ya sha kaye a hannun Ibrahim Yahaya Oloriegbe na APC. Saraki ya kasance gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011.

Hazalika, wani tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, wanda ya yi shugabanci a matsayin Shugaban marasa rinjaye kafin ya sauya sheka zuwa APC a watan Agusta da ya gabata, ma ya rasa kujerarsa. Akpabio ya kasance gwamnan Akwa Ibom tsakanin 2007 da 2015.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments