Saturday

Home Shekaru 30 kensn da kasa na ke wanke baki - Mazaunin Kano
Wani dattijo mazaunin garin Kano mai suna Malam Isah Adamu ya ce ya kwashe a kalla shekaru 30 a rayuwarsa ba tare da amfani da buroshin goge baki ba tun bayan bacewar wanda aka taba saya masa a baya.
Da kasa nake anke hakori

A hirar da Malam Isah ya yi da Bbc, ya ce duk wayewan gari ya kan tara kasa ya zuba a bakinsa ya goge kuma hakan na fitar masa da daudar da ke cikin bakinsa.

"Na gamsu da wannan hanyar ta amfani da kasa wurin tsaftace baki na kuma mutane ba su kukan cewa bakina na wari, " a cewar Malam Isah.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

A halin yanzu shekarun Malam Isah na haihuwa sun kai 70 kuma yana sana'ar gadi ne a garin Kano.

Lamarin wannan dattijon ya sanya majiyar Legit.ng ta tuntubi wani likitan hakora mai suna Dakta Idris Ado da ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Aminu Kano da ke garin Kano.
Dakta Ado ya ce ya dace Malam Isah ya rika gauraya kasar da ya ke amfani da ita wurin wanke bakinsa da gishiri saboda gishiri na kashe kwayoyin cuta masa haddasa matsala a jikin dan adam.

DUBA WANNAN : Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna.

"Abinda Malam Isah ke aikatawa ba za a ce ya yi laifi ba domin akwai wasu da ke amfani da kasar ko gawayi wurin goge baki amma ya dace a rika gaurayawa da gishiri saboda kashe kwayoyin cuta. Ya kuma shawarce shi ya rika amfani da asuwaki wurin goge harshensa domin harshe ne mattatarar kwayoyin cuta a cikin bakin dan adam," inji Dakta Ado.

Dakta Ado ya kuma shawarci al'umma su rinka ziyartar likitan hakori a kalla sau biyu a shekara domin a duba lafiyar hakoransu saboda ba duka kwayoyin cuta bane goge baki da buroshi ke iya gusarwa.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments