Thursday

Home Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe
Shugaban jam’iyyar APC na kungiyar Fulani a fadin kasa, Alhaji Shehu Aliyu ya bayyana cewa masu sauya shekar sun bar tsohuwar jam’iyyar su ne saboda sakacin shuwagabannin PDP, sannan ya kara da cewa a halin yanzu alúmman Fulani na fuskantar barazanar rashin isasshen wuraren kiwon dabbobi.

Yace shuwagabannin tare da magoya bayan su sun yanke shawaran hada kai da APC, tare da gudanar da ayyuka don tabbatar da nasarar yan takaranta a lokacin zabbukan gwamnoni da yan majalisan jiha.

Shugabannin Fulanin PDP 66 da mabiyansu 1000 sun koma APC gaab da zabe
Yayin da yake magana, shugaban kwamitin dattijan APC, Alhaji Aminu Tambari Tafida, ya sha alwashin cewa za a biya wa Fulanawa bukatunsu idan Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto da Faruk Malami Yabo suka yi nasara a zabe, In sha Allah.

Shugaban jam’iyyanr a na jihar, Alhaji Isah Sadiq Achida, yayi kira ga yan Fulani a fadin jihar da su fito kwansu da kwarkwatan su a ranar Asabar don zaban yan takarar jam’iyyar.

Alhaji Isa Sadiq Achida ya sha alwashin cewa gwamnati wacce APC ke jagoranta za ta mayar da hankali a matakai da zasu biya wa Fulani da dabbobin su bukatun su.
No comments:
Write Comments