Tuesday

Home Tofa - An kayyade kudin sadakin aure a kafatanin kasar nan
Wani babban Malamin addinin Musulunci a kasarnan, Dr Abdulhameed Shu'aib Agaka, ya bayyana N13,438 a matsayin ainahin kudin sadakin aure a addinin musulunci.

Nawa ne sadakin aure, sadakin aure

Sannan ya kara da cewa, addini ya halatta, idan miji yana da hali ya biya fiye da yanda shari'a ta bayyana.

A lokacin da yake bayani, a gidan radiyo a garin Ilorin dake jihar Kwara, Dr. Agaka, wanda yake tsohon Malami ne a jami'ar Bayero dake Kano, yace duk wani aure da aka yi shi ba tare da an biya sadaki ba, to bai hallata ba a musulunci.

KU KARANTA: (Music Mp3) - Uban Abba Zama Daram - New song by Rarara&Ado gwanja - Download now.

Miji shine yake bada sadaki ga mata, domin nuna girmamawa a gareta, da kuma kara bada tabbacin cewa duk wasu lamura nata sun dawo kanshi.

Sannan ya kara da cewa a musulunce ana iya amfani da shanu, filaye, gonaki, zinare da wasu abubuwa dai masu muhimmanci wurin biyan sadaki.

A karshe Malamin ya shawarci Musulmi da su dinga bin dokar da Allah da Manzonsa suka gindaya, musamman ma ta fannin aure, domin kaucewa zinace-zinace.
No comments:
Write Comments