Tuesday

Home Tsaffin Jakadun Najeriya sun nemi a soke maimacin zaben gwamnan wata jiha a Arewa, sun fadi abinda zai haifar
A yau Talata kungiyar Jakadun Najeriya reshen jihar Benuwe, ta jaddada bakuta gami da muhimmancin soke maimaicin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 23 ga watan Maris kamar yadda hukumar zabe ta kayyade.

Da ta ke gabatar da jawabai yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Makurdi, kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga cikin lamarin maimaicin zaben gwamnan jihar Benuwe da ka iya tayar da zaune tsaye cikin ta da kuma kasa baki daya.

DUBA WANNAN : Ainihin abin da ya sa Sarkin Yakin Atiku yake shirin barin Jam'iyyar PDP.

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Canada da kuma Mexico, Ambasada Iyorwuese Hagher da ya yi jawabi a madadin sauran tsaffin Jakadu hudu na jihar Benuwe, ya gargadi shugaba Buhari akan gaggawar shiga tare da yin ruwa da tsaki cikin zaben jihar Benuwe domin gudun da na sani.

Ba ya ga kira na neman soke maimacin zaben gwamna, kungiyar a nemi shugaba Buhari da ya shawarci hukumar INEC kan tabbatar da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom a matsayin wanda ya yi nasara yayin zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Kungiyar ta yi tuni da cewa, kasancewar su jakadu akwai bukatar shugaban kasa Buhari ya yi azama wajen kare martaba da kuma 'yancin al'ummar jihar Benuwe ta hanyar ba su dama wajen zaben shugabannin daidai ra'ayi domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KARANTA KUMA: Jami’in kwastam da yaki karban cin hancin naira miliyan 152 ya samu karin girma (Hotuna) .

Bayan zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, gwamna Ortom na jam'iyyar PDP ya samu gamayyar kuri'u 410,576 yayin da abokin adawar sa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime ya samu kuri'u 339,022.

A yayin da akwai tazara ta kimanin kuri'u 81,554 a tsakanin su, hukumar zabe ta ce zaben bai kammala ba a sanadiyar adadin kuri'u 121,019 da ta soke da ka iya sauya sakamakon sa tare da kaddamar da hukuncin maimaici a wannan mako.
No comments:
Write Comments