Saturday

Wata kotu a kasar Iran ta yankewa wata yar fafutukar kare hakkin bil adama hukucin bulalai 148 da zaman gidan kurkuku na tsawon shekaru 38 sakamakon yadda take yaki da sanya Hijabi a kasar ta hanyar da'awar wayewar kai.

Mijin matar mai suna Reza Khandan, wanda ya garzaya shafin ra'ayi da sada zumuntar Facebook domin bayyanawa duniya halinda uwargidarsa ke ciki. Ya wallafa cewa matarsa mai suna Nasrin Sotudeh, na tsare hannun hukuma bisa ga zargin kyamar hijabi.

A yanzu haka, kotu ta yanke mata hukuncin shan bulalai 148 sannan zaman gidan wakafi na tsawon shekaru 38.

KU KARANTA: Yan asalin jihar Kano mazauna Amurka da Turai sunce suna tare da Ganduje

A cewarsa bai san iya adadin shekarun da za ta yi a kurkuku. Saboda hirarsa da Nasrin na dan kankanin lokaci ne. Basu samu damar yin dogayen bayanai ba. Amma tana garkame a yanzu haka a gidan wakafin Evin,ta sanar musa cewa, hukuncin farko, shekaru 5 ne,inda na biyu kuma, shekaru 33 da bulalai 148.

Ana zargin Nasrin Sotudeh da aikata wasu manyan laifuka 7,wadanda suka hada leka sirrukan gwamnatin Iran,yawo ba tare da hijabi ba da kuma da'awar hana matan kasar rufe kawunansu." inji lauyan wacce ake tuhuma.
A shekarar 2012, Tarayyar Turai ta karrama Sotudeh da lambar yabo ta Sakharov sabili da 'yancin bayyana ra'ayoyinta.
No comments:
Write Comments