Thursday

Home Yanzu Yanzu: Kotu ta dakatar da INEC daga sake gudanar da zaben gwamna a Adamawa
Wata babbar kotun jiha da ke da zama a Yola ta bayar da wani umurni da ke dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta daga sake gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa.
Arewa24 labarai, Arewablock.com, arewa24, Arewa24 wakoki

Justis Abdulaziz Waziri na kotun jihar ya bayar da wannan umurni ne bio bayan wata kara da jam’iyyar Movement of Restoration for Defence of Democracy (MRPD), ta shigar wanda ke ikirarin cewa an cire logon jam’iyyarta daga takardar zaben gwamna day a gudana a ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai wani lauya, Sunday Wugiri ya fada ma jaridar Sahara Reporters cewa “koda dai wannan umurnin na da inganci a yanzu, kotu bata da hurumin gabatar da shi.

An kuma tattaro cewa a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi Gwamna Jibrilla Bindow da shirin amfani da MRPD wajen juya zaben da za a sake gudanarwa.
No comments:
Write Comments